Kasuwa na inganta ƙwarewar 'yan noma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma. Yana baiwa kowa damar samun bayanai, kasuwanni, tallafin kuɗi, da kuma damammaki cikin sauƙi. Manufar Kasuwa ita ce magance manyan matsalolin da ke damun fannin noma.
Kasuwa ne sabon gurbi na zamani da aka kirkira musamman don saukaka harkokin kasuwancin noma ga kowa da kowa. Yana kawo mafita ta musamman ga manoma, yan kasuwa, da masu saye, ta hanyar hada su wuri guda domin gudanar da cinikayya mai inganci da riba. An tsara shi ne don kawar da matsalolin samun kasuwa, yana bude sabbin hanyoyi na tattalin arziki a fannin noma. Da Kasuwa, cinikin kayan gona ya zama mai sauki da kuma sauri fiye da da.
Wannan dandali na zamani yana baka damar shiga kasuwanni masu yawa da inganci ba tare da wahala ba, inda zaka iya haduwa da masu buqatar kayanka ko kuma samun kayan da kake nema cikin sauki. Tare da Kasuwa, kana da damar samun labaran kasuwa na ainihin lokaci, gami da farashin kayayyaki daga wurare daban-daban a fadin qasa, wanda hakan zai baka damar yanke shawara mai kyau da kuma cin riba mai yawa. Bugu da kari, an samar da tsarin biyan kuɗi mai sauri da aminci, wanda zai baka damar kammala hada-hadar cinikinka cikin lokaci kankani.
Ba wai kawai haka ba, Kasuwa yana baka damar bibiyar oda ko isar da kayanka tun daga farko har zuwa lokacin da suka isa hannun mai buqata. Wannan fasaha tana baka kwanciyar hankali da tabbacin cewa komai yana tafiya daidai. Idan kuma kaga kana buqatar taimako ko bayani, akwai sashin kula da kwastomomi wanda ke aiki awa 24 a rana, kwana 7 a mako. Ko da yaushe, akwai mutanen da za su kula da bukatunka. Kasuwa ne abokin tarayya mai cikakken bayani don bunkasa harkokinka na noma.